Mark 5

Warkar da Mutum Mai Aljanu

1Suka ƙetare tafkin suka je yankin Gerasenawa. 2Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. 3Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya ɗaure shi, ko da sarƙa ma. 4Gama an sha ɗaure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yǎ kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yǎ riƙe shi. 5Dare da rana, sai yǎ dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai.

6Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. 7Ya yi ihu da babbar murya, ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” 8Domin Yesu ya riga ya faɗa masa, cewa, “Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”

9Sai Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Mene ne sunanka?”

Sai ya amsa, ya ce, “Sunana Legiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.”
10Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yǎ kore su daga wurin.

11A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. 12Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” 13Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.

14Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. 15Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. 16Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. 17Sai mutane suka roƙi Yesu yǎ bar yankinsu.

18Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yǎ bi shi. 19Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.” 20Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis
Wato, Birane Goma
a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

Yarinya da Ta Mutu da Mace Marar Lafiya

21Da Yesu ya sāke ƙetarewa cikin jirgin ruwa zuwa ɗaya hayen tafkin, sai taro mai yawa ya taru kewaye da shi yayinda yake a bakin tafkin. 22Sai ɗaya a cikin masu mulkin majamiʼa, wanda ake kira Yayirus ya zo wurin. Da ganin Yesu, sai ya durƙusa a gabansa, 23ya roƙe shi da gaske, ya ce, “Ƙaramar diyata tana bakin mutuwa. In ka yarda, ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, domin ta warke, ta kuma rayu.” 24Sai Yesu ya tafi tare da shi.

Babban taron kuma ya bi shi, suna ta matsinsa a kowane gefe.
25A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. 26Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. 27Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, 28domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.” 29Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.

30Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”

31Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”

32Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yǎ ga wa ya taɓa shi. 33Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. 34Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”

35Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majamiʼa, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”

36Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majamiʼar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”

37Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗanʼuwan Yaƙub. 38Da suka iso gidan mai mulkin majamiʼar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. 39Sai ya shiga ciki, ya ce musu, “Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.” 40Sai suka yi masa dariya.

Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take.
41Sai ya kama hannunta ya ce mata, “Talita kum!” (Wato, “Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”) 42Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya, (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai. 43Sai ya ba da umarni mai tsanani, kada kowa yǎ san kome game da wannan. Sai ya ce musu, su ba ta wani abu ta ci.

Copyright information for HauSRK